Kwankwaso zai janye takarar sa
Maigirma dan takaran Shugaban Kasar Nigeria a jam'iyyar NNPP Sen. Rabiu Musa Kwankwaso ya amsa gayyata zuwa Kasar Burtaniya cibiyar tattauna abubuwan da suka shafi hulda da kasashen duniya na Kasar Burtaniya wato
''British Chatham House''
An yiwa Kwankwaso tambayoyi game da takaran Shugabancin Najeria da yake nema, har da rashin tasirin da yake dashi a yankin Inyamurai da kuma Yarabawa wanda gashi har an kusa rufe kamfen amma Kwankwaso bai fara a yankin kudu ba, kuma kuri'un 'yan Arewa kadai ba zai kaishi kujeran Shugabancin Nigeria ba.
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
A tattaunawar da turawan Ingila sukayi dashi a Chatham House, yace a shirya yake ya janye daga takaran Shugaban kasa ya marawa wanda yake ganin ya cancanta baya indai yana da kwalitin daya fishi na kawowa ƙasa cigaba da samarwa da Talakwa sauƙi mai ɗorewa.
To anan ya kamata Kwankwaso ya duba makomar Arewa, ina da fahimtar cewa bai kamata a samu wata Gwamnatin tarayya wanda babu Kwankwaso a cikinta ba, saboda Kwankwaso mutumin kirki ne mai kishin Arewa, kamar yadda ya fada cewa zai iya janye takarar sa ya mara wa wani baya to ya kamata ya duba makomar Arewa.
Kwankwaso ya san ta'adi da ta'addancin da Tinubu ya yiwa 'yan Arewa shekaru 22 da suka gabata lokacin da yake Gwamnan Lagos, kuma Kwankwaso ya san ta'adin da Peter Obi ya yiwa 'yan Arewa lokacin da yake Gwamnan Anambra, wanda a lokacin Kwankwaso yana Gwamnan Kano har tattaki yayi zuwa Anambra inda da kansa ya daukarwa Æ´an Arewa Lauyoyi don su kare su a wajen shari'a.
Muna kyautata wa Kwankwaso zato na alheri a matsayinsa na mai kishin Arewa ba zai goyi bayan takaran mutanen da akwai alhakin jinin 'yan Arewa a tafin hannunsu ba ko da zasu bashi dukkan kudin da suka mallaka
Allah Ka taimaki Kwankwaso, Ka bashi ikon zartan da hukunci mafi alheri agaremu.