A hukumance kamar yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana Agba a matsayin Wanda ya lashe zaɓen gwamna na wannan shekarar amma da ƙuri'ar da bata gaza dubu 3 uku ba. Wannan dai shine Karon farko da Musulman jihar Taraba suka nunawa duniya cwwa suna da yawa a jihar kuma suna da iko na zaɓarusulmi a jihar ta Taraba domin bata taɓa yi ba kuma baza tayi ba kamar yadda T.Y Ɗanjuma yasha alwashin cewa idan yana raye babu wani musulmi daya isa yaci mulki a jihar indai yana numfashi a doron ƙasa ba don komai ba sai don irin ƙarfin da Allah yai masa a jihar kuma yake iya juya kowa da komai na jihar, don ko gwamnan dake kai yanzu akwai qata majiyar data bayyanawa Jaridar Raihana cewa ƙanin yayar sa ya dauko daga jiahat kaduna ya ɗora shi a kujerar gwamna kuma mutane suka karɓe shi kamar yadda ya saba, mqjiyar ta ƙara da cewa sau da dama yakan je jihar kadun yainta musu aikin titina kuma ance bai taɓa kwana a cikin gidan gwamnatin Taraba ba, son ance El-Rufa'i ya taɓa yi masa gori kan yaje ƙasar sa ta Taraba yai musu aiki domin suna cikin buƙata, ba yaje yana aiki a ƙasar da ba tashi ba.
Sai dai wannan karon alwashin sa ya kusa karyewa kasancewar anyi zaɓen shugaban ƙasa a ƙasar kuma kiristocin jihar sun nuna ƙabilancin addini inda suka zaɓi Peter Obi a matsayin shugaban ƙasa duk da ya kawo musu tallar ATIKU kamar dai yadda kowane kirista yayi a najeriya bahaushe ko sauran yaruka. Da ganin wannan yasa suma musulman jihar suka fito suka nuna ƙwanjin su inda suka zaɓi nasu Musulmi wato Prof. Muhammad a matsayin wanda zai gaji gwamnan jihar wanda a tarihi tun bayan da BABA SUNTAI ya rasu mataimakin sa ya karɓa wanda kuma ya kasance musulmi basu taɓa yin gwamna musulmi ba , sai dai haƙan su bai cimma ruwa ba.