Yanzu Haka Wani Matashi Ya Hau Saman Ƙarfen ARTV Kano Yace In Baa Biyashi 500k Da Banki Suka Cinye Masa Ba Zai Faɗo Ya Kashe Kansa
Wani Matashi a jihar Kano mai suna Saifullahi ya hau saman ƙarfen gidan talabijin na Abubakar Rimi ARTV Kano dake Hotoro, kan cewa indai ba'a biya shi kudin da banki suka cinye masa ba Saiya faɗo.
Jaridar Amintacciya ta rawaito cewa Matashin ya hau ƙarfen ne yau da misalin ƙarfe 2:50PM, inda ya hau ba tare da an sani ba, bayan ya hau ya ce shi bazai sakko ba sai an Biyashi kudin da banki suka cinye masa.
Bayan hawan matashin ya bar Number sa, inda shugabar gidan talabijin na ARTV Hajiya Sa'a Ibrahim ta kirashi take bashi haƙuri kan ya sakko zata bashi kash na kuɗin, sai dai yace shi sai dai tayi masa transfer.
An nemi da ya sakko kasancewar babu network amma yace shi bazai sakko ba, sai yaga alert, inba haka ba, zai faÉ—o ya kashe kansa.
Matashin yace kuÉ—in ba nasa bane, dan haka shi bai san mai zai faÉ—a wa masu shi ba, domin kuÉ—in har kashi uku ne, amma yafi damuwa da wannan dubu É—ari biyar É—in, kuma indai ba'a bashi ba zai faÉ—o ya kashe kansa.
Har yanzu ana cigaba da rarrashin Saifullahi da ya sakko yace sai yaga alert,.