Rahotanni dake fitowa daga jihar kaduna sun bayyana kararara cewa fitaccen jarumin kannywood Adam A Zango ya saki matarsa bayan wata 'yar hatsaniya data shiga tsakaninshi da matarshi mai suna soffy.
Ga masu bibiyar shafukan tsohuwar matar tasa, ansanta da tallata kayan sawa na mata, riguna da jakankuna a shafukanta na sada zumunta kamar Facebook da instagram.
Sai dai anwayi gari da rahoton dake nuni da cewa Adam zango ya saki matarsa bayan ta wallafa hotonta a shafinta na TikTok.
Zango dai yayi kaurin suna wajen sakin yan mata wanda wasunsu daga masana'atar yake auransu,
Cikin jaruman daya aura har da fatima wadda ta haifa masa Haidar, da maryam Nass wacce akafi sani da maryam Ab yola, itama dai tayi aurenta a kwanakin baya.
To sai dai Soffy ce wanda basu hadu ba a film har ta kaisu ga aure suka haifi diana.
Zango ya bayyana hujjojinsa na sakinta, ciki har da sakin hotonta datayi a kafar TikTok.
Kazalika yace tana terere dashi a duniya da cewa baya bata abinci kuma baya kula da danginsa.
Kazalika zango yace ko sana’ar saye da sayarwa da aka ga tanayi shi ya bata jari, amma yanzu nema take tafi karfinsa.
Zango yace, idan anzabi sana’ar datake akan aurenta shikenan
, amma idan aka daidaita shima lafiya lau, acewarsa yajima yana hakuri da ita, duk da dai ita ma tanayi dashi.
Zango dai yace yana ganin bazai kara aure ba a duniya.