Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana Taofeek Ajilesoro na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar tarayya ta Ife a ranar Asabar.
Jami’in zabe na INEC, Farfesa Abdulfatai Makinde ne ya bayyana Ajilesoro, wanda ya samu kuri’u 53,078 a matsayin wanda ya lashe zaben a babban dakin tattara sakamakon zaÉ“e na Ife a yau Lahadi a Ile-Ife.
Mista Makinde ya ce dan takarar jam’iyyar APC, Benjamin Adereti, ya samu kuri’u 51,051.
Ajilesoro dan majalisar wakilai ne, mai wakiltar mazabar tarayya ta Ife a majalisar wakilai.