Albarkar Da Zakí Samú Lokacìn Da Mijinki Ya Ƙara Aúre:
A duk sati zaki samu kwana uku ko huɗu da zaki kwanta sa'ar da kika ga dama kuma ki tashi sanda kika ga dama ba tare da takura ba.
Babu damuwar lalle sai kin yi girki, duk abin da kika samu zaki iya kaiwa bakinki, hakan zai taƙaita miki yawan wanke-wanke da aikin gida.
Ƙawayenki zasu zo ku yi hira yadda kuke so, haka in ƴan uwanki, zaki samu sakewa sosai.
Duk lokacin da mijinki yazo gidanki; ba shi da buri face ya yi miki abin da zaki ji daɗi, don haka kar ki yadda ki nuna fushinki. Wannan zai ƙara miki lafiya da kuma samun nutsuwa da jin daɗi da walwala.
Ko babu komai kin samu lokacin da zaki huta da yawan karbar umarni (Yi kaza, bar kaza)
In kika fara kallo ko kuma danna waya babu wanda zai ce miki 'Uffan', duniya daɗi, Ki more yadda kike so.
Idan masifaffe kika aura; akwai kwanakin da zaki huta da masifarsa, in kuwa mutumin kirki ne kin ga zai ƙara samun lada, don alherinsa zai ƙara yaɗo, b ya taƙaita guri ɗaya ba.
Ku duba harkar ƙarin aure da idon basira, haƙiƙa a cikinsa akwai maslaharki Hajiya wacce tafi ta mijin yawa.
Me kuke jira, kowacce taje ta matsawa mijinta sai ya ƙara aure. In ya ce bai shirya ba ɗakko kadararki (Gold ko wani Fili da kike mallaka ko kuma jarin da kike kasuwanci ko kuma ribar) ki siyar ki ba shi!
Allah ya baku ikon aikata aikin alheri.
Daga shafin Raihana