Ba a sanya sunan jam’iyyar NNPP, a kan takardar kaɗa ƙuri'a ta zaɓen ƴan majalisar wakilai na karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.
A baya dai jami’an hukumar zabe na INEC a karamar hukumar sun dawo da takardun kaɗa ƙuri'ar da aka riga aka raba zuwa rumfunan zabe, amma daga baya aka raba su bayan sun samu izini daga kwamishinan zabe na jihar.
Ringim dai nan ce ƙaramar hukumar gidan dan takarar gwamna na jam'iyyar, Aminu Ringim.
Wani jami’in zaben da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wannan jarida cewa, takardun kaɗa ƙuri'ar na dauke da tambarin jam’iyyar ta NNPP ne kawai amma babu sunan jam'iyyar.
Sai dai jami’in ya ce za a gudanar da zaben duk da cewa babu sunan jam'iyyar.
Haka kuma makamancin hakan ya faru a jihar Ondo, inda aka cire tambarin jam’iyyar Labour Party, LP a cikin takardun kaɗa ƙuri'a da aka aika jihar.
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga INEC da ta ɗage zaben a majalisar wakilai bakwai da kuma na sanata guda daya a fadin jihar, har sai an yi abin da ya kamata.