Hadin guiwar jami'an tsaron Soje, yan sanda, jami'an tsaron farin kaya sun kama ciyaman din Ungogo Engr. Abdullahi Ramat da na Rimin Gado Hon. Munir Dahiru dauke da bundigu inda ake zargin sun jagoranci yan daba wajen kaiwa tawagar dan takarar Shugaban kasa na jam'iyyar NNPP Sanata Rabi'u Kwankwaso.
Jaridar DailyNigeria ta rawaito cewa jami'an tsaro sun kwace bundigun inda a yanzu suka wuce da su sashin binciken manyan laifuka na rundunar yan sandan Kano.