An kashe mutum ɗaya a cikin siyasa tsakanin ƴan APC da PDP a Jigawa
Rundunar ƴansanda a jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum daya a wajen taron siyasa na ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Mustapha Sule Lamido.
Lawan Shiisu, kakakin rundunar, wanda ya bayyana hakan a jiya Asabar a wata sanarwa, ya yi zargin cewa magoya bayan PDP ne suka kashe mamacin.
Mista Shiisu, mai muƙamin DSP, ya bayyana cewa, marigayin, mai suna Abdullahi Isyaku mai shekaru 37, an kashe shi ne lokacin da faɗa ya ɓarke tsakanin magoya bayan jam’iyyar PDP da APC a Ƙaramar Hukumar Maigatari.
“A ranar Juma’a da misalin karfe 6:20 na yamma, yayin da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP ke gudanar da yakin neman zabe a karamar hukumar Maigatari, yayin da suka isa sakatariyar APC, sai rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan jam’iyyun.
"Kuma sai ƴan barandan Santuraki (Mustapha Sule Lamido) sun kai hari kan wani Abdullahi Isyaku mai shekaru 37 kuma mazaunin Gangare da ke garin Maigatari," in ji Mista Shiisu.
Mista Shiisu ya ce an kama mutane biyar da ke da alaka da lamarin.
Sai dai ya koka da yadda marigayin, wanda tun farko aka garzaya da shi babban asibitin Gumel, ya rasu a lokacin da ake kokarin yi masa magani.
PPRO ɗin ya bayyana cewa, an fara gudanar da bincike a sashin binciken manyan laifuka na rundunar da ke Dutse.