Shugabanni 73 na ƙungiyar izala sun bayyana goyon baya ga Atiku, inda Sheikh Jingir ya zaɓi Tinubu
ƘungiyarJama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah, JIBWIS, ta amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Kafin amincewar, kungiyar ta gudanar da zaÉ“en cikin gida, inda Atiku ya samu kuri'u 73 a kan jam’iyyar APC, dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, wanda ya samu kuri’u 13.
Jaridar Raihana ta ruwaito cewa, shugabannin sassa 115 ne su ka halarci muhimmin taron yanke shawara, yayin da 19 su ka ki kaÉ—a kuri’a, su ka ce za su bi zabin shugaban Æ™ungiyar na Æ™asa, Sheikh Sani Jingir.
Bayan bayyana sakamakon, Jingir ya amince da takarar Tinubu da Shettima, wa ce haÉ—aka ce ta Musulmi da Musulmi, amma ya umurci mabiyansa da su kada kuri'a ga wanda su ke da ra'ayi..
“Da sunan Allah, ina mai mutunta ra'ayin ku, kuma ina rokon ku da ku zabi ra'ayin ku domin hakan ma daidai ne a gare ni," in ji shi.
“A gare ni, wannan ba shine karo na farko ba, kuma kuna sane da hakan. Amma zan zabi tikitin musulmi da musulmi. Zan zabi Tinubu, kuma ku zabi ra'ayin ku.”