Wasu karuwai a babban birnin tarayya, FCT, Abuja sun koka kan rashin ciniki a kasuwancinsu sakamakon karancin tsabar kuɗi a hannun kwastomomi.
Wasu daga cikinsu da su ka zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja a yau Lahadi sun ce ƙarancin tsabar kuɗi na zama barazana kuma ya gurgunta kasuwancinsu.
Sun ce duk da cewa manufar musanya kudi abin yabawa ne, amma yadda ake aiwatar da ita a halin yanzu kalubale ne ga kasuwancinsu.
Karuwan sun ce abokan cinikin su sun ragu sosai saboda halin da ake ciki na rashin tsabar kuɗi.
Sun bayyana yanayin a matsayin abin takaici da tafiyar hawainiya ga kasuwancin su.