AREWA MU FARKA......!
Tattaunawa ta musamman tare da
Hon. Rabi'u Baba Nabegu da jaridar Raiha ana.
ME ZAKA CE DANGANE DA HALIN DA ƳAN AREWA SUKA SHIGA SANADIYAR WANNAN CANJI NA SABON TSARIN GUDANAR DA RAYUWA DA GWAMNATI TA FITO DASHI???.
''Ya kamata Al'ummar AREWA mu farka, musan cewar yanzu fa a ƙarni na Ashirin da ɗaya muke, tuntuni duniya ta canza kuma anyi mana nisa sosai, domin an daɗe da barinmu a baya ta fannoni daban-daban, mussamman fannin cigaban kimiyya da fasaha da harkar "Digital economy"
Wannan tsarin da akazo dashi na Cashless policy ko munso ko munƙi nan gaba sai anyishi a wannan kasar kuma kowacce jam'iyya ce a mulki, domin rayuwa kacokan da zamani take tafiya, mu daure mu wayar da kan Al'umarmu yadda zasuyi amfani da banki a wayoyinsu yafi muyita siyasantar da abin nan domin neman kuri'ar jam'iyyar da mukeso, ita jam'iyyar da kake so ka san tsarin da zata kawo nan gaba ne? Dole fa muzauna muringa tunani mai zurfi akan abubuwa, bazai taɓa yiwuwa aita tafiya a wuri ɗaya ba a wannan duniyar ko Kuma yadda muke so, muna cikin (Digital world) ne fa yanzu, musaba da chanji da kuma karbar canji a lokacin da yazo shine kawai mafutarmu domin akwai tsare-tsare da dama da nan da wasu shekaru kaɗan zasuyi ta zuwa a zamanance Kuma ba yadda muka iya dole mu tafi da su.
Yanzu Gashinan an shiga halinda kowa yake É—anÉ—ana kuÉ—arsa damu masu bankin da waÉ—anda basu dashi dan ko kana da banki wanda za kai siyayya a wurinsa dole shima sai yana da Banki.
Wasu ma yadda suke mu'amalantar sabon tsarin kamar basu da tunani ba
yanzu fa Abin takaici common NIN NUMBER sai kaga mutum yakai 30 years bashi da Shaidar zama É—an kasa ko katin zabe Talkless of Bank Account ko BVN haba? idan kaga ana rububin abu a AREWA to Kudi za'a samu ko tallafi daga Gwamnatin Tarayya amma bama yin tunani a kan yiwa kan mu abubuwa da suka zama dole kafin a nema a wajen mu''
''A ƙarshe ina son in faɗawa al'umma ƴan'uwana ƴan arewa da mu tashi daga barcin da muke mu sani cewa bacci aikin kawai ne.''
Alh. Rabi'u Baba Nabegu