Ƙarya Naziru Sarkin Waƙa yake babu wanda ya bashi miliyan ɗari da hamsin don ya bar tafiyar Atiku cewar Dauda Kahutu Rarara
Rarara ya faɗi haka ne a wata zantawa da sukai da jaridar DW ta hanyar allon gani gaka. inda ya bayyana cewa babu wanda ya baiwa Naziru M Ahmad Miliyan ɗari da hamsin kamar yadda ya faɗa wai don a a rinjaye shi a kan ra'ayin sa inda yace ko Ɗantakarar nasa Atiku Abubakar aka baiwa wannan kuɗin ba zai juya baya ba sai ya karbi wannan kuɗin domin ba ƙananun kuɗaɗe bane, saboda haka ya faɗi wannan zancen ne a tunanin sa shirin film ɗin labari na ake ɗauka ba a zihirin gaskiya ake ba.