Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya shirya kawo ziyara jihar Kano a ranar 9 ga watan Fabrairu.
Sule Ya’u Sule, Kakakin Sanata Ibrahim Shekarau ne ya bayyana haka a yau Laraba a yayin taron manema labarai a sakatariyar PDP a Kano.
Sule ya bayyana cewar Atiku zai zo Kano ne da tawagar yakin neman zaben sa.
Haka kuma a yayin ziyarar zai buɗe makarantar Al’Quran maigirma a unguwar Gunduwawa wanda tsohon gwamnan Kano Sanatan Kano ta Tsakiya Malam Ibrahim shekarau ya gina.
Ya ƙara da cewa munufar wannan makaranta itace don koyar da Al’Qurani da karanta shi da kuma haddar sa cikin watanni shida.
“Hakan zai samar da haziƙan ɗalibai masu kananan shekaru maza da mata da kuma samun guraban karatu a jami’o’in kasar nan.”
Ya kuma ce a ƙalla Makarantar tana da dakunan kwanan dalibai kimanin 500