har kullum idan aka gansu kusa da Talakawa to fa neman ƙuri'a ne ya kai su ko makamancin haka. Basa rayuwa da Talakawa basa ƙaunar kusantar inda suke ballantana su bar iyalansu su kusanci inda suke.
Idan za muyiwa kan mu karatun ta nutsu tun wuri muyi idan ko ba haka ba muna ji muna gani zamu faɗa hannun maƙiyan mu da kan mu kuma mu shiga bala'in da baza mu iya fitar da kan mu daga ciki ba sai dai mu roƙi Allah ya gyara mana duk saboda mun zaɓarwa kan mu baragurbi.
Maimakon muzo muna wannan addu'ar muna jin takaici yafi kyau mu kasance muna roƙon Allah ya ƙarawa shugaban mu lafiya ya cigaba da yimana aikin alkhairi da yake mana saboda mun zaɓarwa kan mu shugaba nagari, Saboda haka ku kwantar da hankalin ku muna sane da halin da ake ciki kuma muna nan zamu gyara idan har kun bamu dama kuma Allah yaso, sannan ku daina tunanin cewa zamu marawa waɗancan mutane da basa ƙaunar ku baya.
Muna nan a kan bakar mu kuma damu za ayi zaɓe inshaAllahu''.