Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yayi Allah wadai da wasu kalamai da gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya furta akan batun canjin fasalin kuɗaɗen Naira (N1000, N500, N200) da babban bankin Nigeria CBN yayi.
Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin tattaunawarsa da gidan Talabijin na Liberty, inda yace ko kusa ko alama bazai iya cewa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari "Habu na Habu" ba, domin asali wani mutum ne wanda Marigayi Dakta Mamman Shata, ya yiwa waka, kuma mutumin ba nagartacce bane.
Ya ƙara da cewa, kalamai da suke nuna rashin dattako basu dace ga shugabanni ba, ko da kuwa ba a jam'iyya daya ake ba, domin watarana idan mutum ya zama shugaban ƙasa, ba zaiji dadi shima a gaya masa haka.
Tunda fari dai gwamna Ganduje ne yayi wasu kalamai akan batun canjin kuɗi, wanda ake ciki ya furta kalmar "Habu na Habu" wacce ake zargin kamar shagube ne ga shugaban ƙasar Nigeria Muhammadu Buhari.