Babbar Magana: Akwai yiwuwar reshe ya juye da mujiya domin an fara bincikar mijin Marigayiya data rasu a asibiti bisa rashin kular data samu daga likitoci kasancewar anyi transfer bata shiga ba kuma aka ƙi kula ta saboda ba'a ga alert ba kamar yadda mijin ta yai zargi.
Shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da daƙile cin hanci da rashawa ta jihar kano Barr. Mahmoud Balarabe ya gayyato kowane ɓangare wanda suka haɗar da likitocin da sukai aiki a lokacin ciki har da shigabar asibitin Nasarawar wato Dr. Rahila da shi kansa Mijin Marigayiya da kuma yar jaridar data ɗauki rahoton al'amarin.
Barr. Balarabe ya buƙaci Mal. Bello mijin marigayiya da yayi bayanin abunda ya faru kamar yadda ya shaidawa ƴar jarida da tayi shira dashi ya kuma faɗa sannan suma bangaren likitocin sukai bayanin yadda al'amarin ya kasance inda suka bayyana cewa babu wani abu ko makamancin abunda ya faɗa daya faru na rashin kula matar sa wanda hasali ma babu wanda yace sai an bada kuɗi ko transfer kafin a kula matar sa a daidai lokacin da yake cewa sunƙi kula su sai an biya kuɗi ta akawun kuma baza su karɓi tsaffin kuɗi ba.
Itama shugabar asibitin CMD, Dr. Rahila ta bayyana cewa yar jarida tayi mata ƙazafi domin lokacin data nemi yin shira da ita bata ce da ita komai ba hasali ma ƙaryata al'amarin tayi tace hakan bai faru ba kuma ba'ayi ba illa iyaka tace zata binciki kundi na bayanan waccan mata domin ta binciki abunda ya faru.
Bayan ji daga kowane ɓangare Barr. Mahmoud ya bayyana nashi jawabin ga
manema labarai inda yace :
''A sakamakon tattaunawa da binciken kowane ɓangare mun gano cewa akwai kuskure cikin hada wannan rahoto da yar jarida ta fitar tare da ayyana hakan a matsayin gaggawa wadda bata haifar da komai sai rashin dai-dai domin aikin sheɗan ne kuma yana da kyau mutane su dunga bincike kan duk wani lamari da suka ji kafin daukar mataki kan al'amari ko na menene domin jin gaskiyar lamari da kuma samun dai-daito da baiwa kowane bangare haƙƙin sa kuma muna nan muna cigaba da bincike kan lamarin domin ɗinke bakin zaran kuma zamu ɗauki duk matakin da doka ta tanadar ga duk wanda aka kama da laifi''.