Hukumar da ke umarni da aikata kyakykyawan aiki tare da hani ga aikata mummunan aiki (HISBAH) reshen jihar Kano, ta ce babu laifi a addinin musulunci don uwa ta auri tsohon saurayin 'yarta.
Jawabin hakan ya fito ne daga mataimakin Kwamandan hukumar a bangaren ayyuka na musamman, Hussaini Ahmad, yayin da yake bayanin Rahoton kwamitin da aka kafa akan wata mata mai suna Malama Khadija daga karamar hukumar Rano, wacce ta auri saurayin 'yarta bayan mutuwar aureta ta mijinta, abinda yan uwanta suke ganin abin kunya ne kuma bai dace ba.
Hukumar HISBAH reshen karamar hukumar Rano ce ta daura auren Khadija da wancan saurayi da 'yarta mai suna Aisha ta ce bata so, amma kuma tace babu laifi ko kadan a lamarin auren a musulunci, domin sai da aurenta ya rabu da tsohon mijinta kuma tayi zaman Iddah na watanni uku kafin ta auri wannan saurayi.
A nasa bangaren, babban kwamandan hukumar na jihar Kano, Muhammad Harun Ibn Sina, ya yaba da aikin kwamitin, ya kuma ja hankalin mutane da su guji yaɗa labarai marasa tushe, musamman akan abinda ya shafi aure, zamantakewar iyali da sauran rayuwar mutane, yafi kamata ma ace mutane sun nemi ilimi akan abinda ya shafi Addini.