''Duk wasu da suke iƙirarin ƙwatar mana zaɓe su dena domin wannan karan lokaci ne na matasa kuma dole a haƙura a basu kuma duk girman layar mutum dole ne ya kiyayi mai zamani''.
Ko me yasa Hon. Lawan yake wannan batu??
''Akwai wasu jam'iyyu da suke tunanin babu wanda zai iya cin mulki idan basu ba kuma babu wanda ya isa yin qani abu idan ba su ba, sannan suna iƙirarin koda wasu sunci zaɓe zasu bi duk wata hanya domin ƙwatar wannan zaɓe saboda haka anyi a baya kuma baza mu ƙara yarda a kuma ba. A ƙarshe ina mai shedawa ɗumbin matasa magoya bayan tafiyar mu ta YPP dasu cigaba da jajircewa wajen yaɗa manufar mu ta alkhairi sannan a fito a dangwala kuri'u ranar zaɓe domin mu kada wanda basu san muhimmancin matasa a siyasa ba.