Hukumar yan sanda ta jihar Kano, ta ce ta hana zirga-zirgar ababen hawa a fadin Kano, daga karfe 12 na daren yau Juma'a zuwa karfe 6 na yammacin ranar Asabar (wato ranar zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisar tarayya).
Kakakin hukumar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka yayin wani atisaye da jami'an yan sanda suka gudanar yau a shalkwatar hukumar dake Bompai Kano, inda yace ba'a yarda wanda ba zaɓe zaiyi yazo wajen zaɓe ba.
Kiyawa ya gargadi al'ummar jihar Kano, akan su bada hadin kai wajen gudanar da zaɓe cikin koshin lafiya, kada a dauki makami ko a sanya wani abu da yake nuna shaidar alamar wata siyasa.
Har ila yau, Kiyawa yace a sanya idanu da zarar an lura da wani motsi ko hanzari da ba'a yarda dashi ba, ayi ƙoƙarin sanar da jami'an tsaro.