Iyalan Marigayi Alhaji Ibrahim Kunya, wanda tsohon kwamishina ne a gwamnatin jihar Kano, a wani lokaci da ya shude, sun ce Jarumar barkwancin nan ta shafin TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ba ta cikin zuri'arsu, basu da wata alaƙa da ita.
Guda cikin 'ya'yan Marigayin mai suna Alhaji Abubakar Ibrahim Kunya, yace suna ne dai yazo daya da kuma wajen zama, lamarin da yasa mutane ke kiransu har a waya suna yi musu maganar Murja, shi yasa suka dacewar su fito su barranta kansu da ita.
"Ina sanar jama'a, Murja Ibrahim Kunya, bata da alaka ko yan uwantaka da zuri'ar Marigayi Alhaji Ibrahim Kunya, kamar yadda wasu suke dauka, don haka zuri'ar Marigayi Alhaji Ibrahim Kunya suke nesanta kansu daga tunanin da wasu ke yi na alaƙa da wannan mata, a karshe muna yi mata addu'ar samun natsuwa da kuma mutunta kanta a matsayinta na yar uwa musulma."
Yanzu haka dai Murja Ibrahim Kunya, na gidan gyaran hali bisa ajiya da kotu da kai ta, kafin a dawo a cigaba da Shari'a,biyo bayan tuhumar da ake mata na yada kalaman batsa, zage-zage, rashin tarbiyya da sauransu.