Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tsinewa gwamnonin jihohin Bayelsa da Edo, bisa yadda yace sun goyi bayan ƙin ƙara wa'adin daina amfani da tsofaffin kuɗaɗen Naira (N1000, N500, N200) da babban bankin Nigeria CBN ya canjawa fasali.
Ganduje yace gwamnonin APC sun kai ƙara kotun Koli domin hana CBN daina amfani da tsofaffin kuɗaɗe, amma abin mamaki gwamnonin Edo da Bayelsa suka ce suna goyon baya.
Hakazalika yace, NNPP tace masa baiyi daa'a ba, saboda yace gwamnatin tarayya bata kyauta ba, yace sunfi so kawai al'umma su cigaba da shan wahala.