Majalisar wakilai ta ƙasa, ta ce babu lokacin daina karɓar tsofaffin kuɗaɗen Naira da babban bankin Nigeria CBN, karkashin jagorancin Godwin Emefiele, ya canjawa fasali (N1000, N500, 200) da za'a daina amfani da tsofaffin kuɗaɗen daga ranar 10 ga watan Fabrairu.
Bayanin hakan na kunshe cikin sanarwar bayan taro da majalisar ta fitar, bayan wani zama da akayi tsakanin kwamitin da aka kafa bibiyar harkokin kuɗi, karkashin jagorancin dan majalisar Doguwa da Tudun Wada daga jihar Kano, kuma shugaban masu rinjaye na majalisar, Alasan Ado Doguwa
Sanarwar ta ce, majalisar da kuma CBN, duk sun amince akan cewa babu ranar daina karɓar tsofaffin kuɗaɗe, sannan kuma majalisar da umarci Emefiele
ya bada umarnin sakin sabbin kuɗi a bankuna da injin cirar kudi na ATM, domin a samu yawaitar kuɗin a hannun mutane.