Har yanzu Adamu Zango ya kasa fahimtar cewa shi ɗan ƙauye ne kuma dole ƴr ƙauye ce kawai zata dace da zama dashi a harkar auratayya.
Tun lokacin da Adamu zango ke aure baya duba ƴar asali da kuma inda ta fito shin ta dace dashi ko bata dace dashi ba kawai sai ya nuna shi mai abun hannu ne kuma a bashi mace ya aura bayan ba haka aure yake ba mudamman a ƙasar Hausa.
Zaku gane cewa ba tsarar shi wajen aure yake samu ba shi yasa duk yarinyar daya aura data samu abunda ta nema wato kuɗi sai kawai tanemi ya sake ta ko kuma tayi masa abunda zai ji haushi da kansa ya sake ta.
Adam A Zango Ɗan Ƙauye ne kuma asalin sa Talaka ne mai neman na abinci, wannan tarihin ba zai taɓa gogewa ba kuma duk kuɗin da zai mallaka a duniya ba zai koma ya canza asali da tarihin sa ba. Da zai auri ƴar ƙauye irin sa da ya zauna lafiya kuma ya yiwa Allah godiya a fannin aure, kuna yakasance cikin waɗanda sukarabauta da jin daɗin Duniya. Ya kasa yarda da haka shi yasa kullum yake aure kuma yai saki sqboda da zarar sun samu abunda suka samu sai su nemi a rabu ta kowace hanya.kuma su nemi ɗan birni su aura kuma su zauna dashi. Kuɗi baya canza asali kuma baya canza tarihi duk inda mutum zai je a duniya, a rashin fahimtar sa ne yake neman haramtawa kansa abunda Allah ya halasta masa. ''Wai yana jin ya dena aure.''
Zai ƙara aure nan gaba amma kuma idan har bai auri irin sa ba to zai dawwama cikin nadamar aure a rayuwar sa.
Daga shafin Raihana