Abdulaziz Abdulaziz, Mataimaki na Musamman kan harkokin yaɗa labarai ga ɗan takarar shugabancin ƙasa na APC, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kwarin gwiwa cewa mai gidan nasa ne zai lashe zaɓen yau Asabar.
Abdulaziz ya bayyana haka ne a hira da ya yi da manema labarai bayan ya kada ƙuri'ar sa a mazaɓar sa a yau a Kano.
Ya ce daga yadda su ka zagaya da kuma irin labaran da su ke samu daga wakilan jam'iyyar APC, sun samu kwarin gwiwa cewa Tinubu zai lashe zaɓen da rata mai yawa.
Abdulaziz ya kuma yaba da yadda jama'a, musamman mata su ka fito kwansu da kwakwatarsu domin yin zaɓe.
Ya kuma yaba da yadda ake zaɓen cikin zaman lafiya a Kano da ma sauran sassa na ƙasar.