Dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour Party, LP a jihar Kano, Bashir I Bashir, ya fice daga jam’iyyarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
A ranar 21 ga watan Janairu ne dan takarar gwamnan ya kauracewa taron gangamin jam’iyyar a Kano tare da shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Mohammed Zarewa, kodinetan yakin neman zaben Peter Obi na jihar, Balarabe Wakili da dan majalisar yakin neman zaben shugaban kasa, Idris Dambazau.
Wata majiya da ke kusa da dan takarar ta tabbatar da sauya shekar Mista Bashir da wasu jiga- jigan jam’iyyar LP zuwa APC a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta ce babban dalilin da ya sa suka sauya sheka shi ne na ware manyan masu ruwa da tsaki a Arewa wajen yanke shawara da kuma rashin samun cikakkiyar alkibla kan maslahar Arewacin Najeriya.
An tattaro cewa Mista Bashir ya gana biyu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu da kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a Legas da Abuja inda suka amince da sharuddan sauya sheka.
A cewar wata majiya dan takarar jam’iyyar LP ya amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC tare da yin alkawarin tara masa magoya bayansa.