Da babu kuɗi sai dai abunda ake kira ''ban gishiri na baka manda'' aka koma bada gwal da azurfa, aka kara canza tsarin aka koma bada risiti a ma'ajiya daga baya aka dawo bada takardu wanda duniya ta yarda dasu bayan da aka cimma yarjejeniya, yanzu duniya ta canza tsari an koma tsarin lambobi, dasu zaka biya kuma kayi rayuwa da duk abunda kake so wanda shine tsarin da ake cewa "cashless".
Abunda muke so da al'umma suyi domin kubuta daga bacin rana a wannan zamani shine kowa yaje ya koyi harkar da ake faɗa ta "cashless".
Wannan shi kadai mafita kuma hanyar da za'a samu waraka da kuma fita daga cikin kunci cikin sauƙi.