Babban Bankin Najeriya ya janye batun ci gaba da karɓar takardun kuɗi na N1,000 da 500, bayan a baya ya tabbatar da cewa ya umurci bankuna su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin.
Tun farko, Babban Bankin na Najeriya ta bakin daraktansa na yaɗa labaru, Osita Nwanisobi ya tabbatar da cewar ya bai wa bankuna umurnin ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗi na 1,000 da kuma 500.
Sai daga baya bankin ya fitar da wani takarda É—auke da sa hannun daraktar yaÉ—a labarun na CBN inda yake musanta hakan.
Bayan da aka sake kiran sa domin tantance bayanin, Mr Nwanisobi ya ce bai da abin da zai fada baya ga wannan sanarwa da ya fitar daga baya.