Amb. Ibrahim Waiya sun zauna da shugaban hukumar zaɓe ta kano a babban ofishin su na kano takarda mai ɗauke da bayanan yadda ayyukan ɗaki na sa'ido da tsare-tsare yadda zaɓe ke gudana su kuma baiwa juna shawarwari da makamantan su. Amb. Waiya ya bayyanawa manema labarai cewa suna da tabbaci za ayi zaɓe sahihi duba da yadda hukumar ta gabatar da sabbin tsare-tsaren zaɓe da na'urori wanda kafin a shiga zaɓen anyi gwaji kuma sun gani.
Shima a nashi jawabin shugaban hukumar zaɓe ta kano ya bayyana farin cikin sa tare da yiwa wannan gammaya ta kungiyoyi godiya ta musamman tayadda suke basu gudunmawa da duk wani abu da suke dashi kuma maimakon ace suna biyan su amma basa basu komai dasu da ƴan jarida . ya kuma tabbatar da cewa babu wani abu na kuskure da zai faru yayin gudanar da zaɓe.
A ƙarshe shugaban na INEC ya tabbatarwa da al'ummar jihar kano cewa babu wani maguɗi da zai faru a zaɓen shekarar 2023.