Tsohon Gwamnan Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau yayi kira ga dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya na jam'iyyar NNPP, Sanata Rufa'i Sani Hanga, da ya daina É“ata lokaci da kuÉ—insa a neman kujerar Sanatan Kano ta tsakiya.
Malam Shekarau ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce sunansa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC zata ayyana idan har jam'iyyar NNPP ce ta lashe zaɓen kujerar, ba sunan Hanga ba.
Ya ce, Shugaban Hukumar Zaɓe ya tabbatar masa shi ne ɗan takara, kuma tsawon watanni ya kira Hanga ya sanar da shi hakan saboda ƴan uwantaka.