Hukumar dake umarni da aikata kyakykyawan aiki tare da hani da aikata mummunan aiki (HISBAH) ta jihar Kano, ta samu nasarar kamowa tare da gurfanar mawaƙin nan da yayi shuhura a shafukan sada zumunta, Al'Ameen G-Fresh, a gaban hukumar bisa zargin wasa da Sallah a wani faifan bidiyo da aka ɗauke shi, kuma aka yaɗa a shafin TikTok.
Cikin wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook, tace ta kamo shi ne bisa laifin wasa da Sallah, wanda sashin kai sumame na hukumar suka nemo shi kuma suka miƙawa sashin da'awa na hukumar karkashin jagorancin mataimakin babban kwamandan hukumar, Ustaz Hussaini Ahmad Chediyyar Kuda, bisa umarnin babban Kwamanda Dr Muhammad Harun Ibn Sina, a matakin farko.
Hukumar ta kara da cewa, sunyi masa nasiha da nusantar dashi hadarin wasa da addini tare da shawartarsa da yakoma makaranta don gyara addininsa, inda nan take G-Fresh yayi alkawarin gyara al'amuransa kuma yasaka hannu a takarda idan ya sake aikata hakan, to hukumar Hisbah zata dauki mataki na gaba akansa.