Jahiltar lamarin sukai shi yasa suke ganin laifin sa.
Tun farko kamar yadda doka take Gwamnan banki bai da damar canza koda harafi daya ne a jikin takardun kudi da ƙasa take amfani dashi ba tare da umarnin shugaban kasa ba. Koda sabon gwamnan banki aka canza dole sai takardar sanar da sabon gwamna ta isa banki sannan ake iya canza sunan dake kai kamar misalin canza sunan SUNUSI LAMIDO izuwa GODWIN EMEFIELE.
Dokar ƙasa ta baiwa Shugaban ƙasa damar canza launin kudi izuwa kalar da tafi dacewa kuma ana yin haka duk bayan shekaru 6 ko sama da haka. Amma fa al'ummar gari na da damar sanarwa da shugaban cewa tsarin bai musu ba idan hat sun ga zai dame su saboda haka dole a dubi uzurin al'umma kuma ayi abunda suke so kafin ya zama doka bayan watanni 6 don idan ya kai wata shida babu mai iya canzawa sai ya kai watanni 24 sannan za'a iya zama a majalisa aga yiwuwar canza tsarin.
Daga shafin Raihana