Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya sake yin subul da baka yayin da yake yiwa daliban Najeriya alkawarin cewa zasu shafe shekaru 8 suna karatu a jami’a idan ya lashe zaben shekerar 2023.
Tsohon Gwamnan na Legas yayi bayanin hakan ne a taron gangamin yakin neman zabe a birnin Osogbo ranar Alhamis inda ya ce dalibai su kira shi da shege idan bai cika alkawarin da ya dau kar musu ba.
Mafi karancin shekarun da ake yi wajen kammala karatu a jami’o’in Najeriya dai shi ne shekaru 4.
“Ku kirani Shegs idan ku ka shafe sama da shekaru 8 a manyan makarantu.
Zaku yi shekara 8 a makaranta”, inji Tinubu cikin yaren Yarabanci.
Ba dai wannan ne karo na farko da dan takarar ke yin sakin baki ba mussaman a tarun jam’iyyar APC.