:
Wasu wadanda ake kyautata zaton mayakan kungiyar ISWAP ne sun fara raba wa matafiya tarin tsofaffin takardun kudi a manyan hanyoyin yankin da ke kusa da tafkin Chadi.
:
Rahotanni daga jaridar Daily Trust na cewa mayakan na kokarin kaucewa matakin sauyin tsofaffin kudin da sababbin da babban bankin Najeriya ya kaddamar ne.
:
Jaridar ta kuma ce an ga wasu mayakan a kusa da kauyen Mariri kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Monguno a karamar hukumar Guzamala ta Jihar ta Borno.
:
Mayakan sun kasance sanye da kayan yaki na sojojin Najeriya kuma suna tafiya cikin motocin sulke irin na sojoji.
:
Wani ganau ya ce mayakan sun tsaya a gefen hanyar a karkashin wata bishiya dauke da jakunkuna cike da tsofaffin takardun naira:
:
"Sun tsayar da motar da nake ciki. Sai suka tambaye mu ko Maiduguri za mu, daga nan sai suka raba wa kowane fasinja naira 100,000 na tsofaffin takadun kudin. Mun yi mamaki matuka yayin da suka raba wa kowane fasinja wannan kudin."
:
Wani wanda ya shaida lamarin ya ce: "Mayakan sun gaya mana cewa idan za mu iya zuwa banki ma sauya kudin zuwa sababbin takardun naira, to mu yi haka, kuma sun yi mana addu'ar amfana da kudin."