Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yayi nasara a akwatun zaɓen mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a babban zaɓen shekarar 2023 da aka gudanar a wannan rana ta Asabar.
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa, NNPP ta samu ƙuri'u 99 yayin da APC ta samu 39 a zaɓen shugaban ƙasa, hakazalika NNPP din ta samu ƙuri'u 102, APC 53, PDP 15 a bangaren zaɓen Sanata na yankin Kano ta tsakiya.
Bugu da ƙari, NNPP ta samu ƙuri'u 99, APC 46, PDP 24, a zaɓen dan majalisar wakilai ta ƙasa.