Kwankwaso zai ga soyayyar da bai taɓa gani ba a rayuwar sa ta siyasa. ~ Sunusi Lamido.
Lokacin da yai gwamna na farko a kano daga 1999 zuwa 2003 yayi ƙoƙari amma ƙoƙarin sai ya zama ya saɓa da ainihin tunanin malaman wannan lokacin domin a tunanin su ya biyewa tsohon shugaban ƙasa Obasanjo sun kashe arewa bayan ba haka bane. A ƙarshe sai akayi amfani da addini aka kada shi akaɗaura Sen. Ibrahim Shekarau tun daga shekarar 2003 zuwa 2011 amma sai akai rashin sa'a ya bai yi abunda ya kamata domin waɗanda aka baiwa dama suyi aiki a ƙarƙashin gwamnatin sa sai sukayi handama da babakera kuma yaƙi bibiya a matsayin sa na gwamna. Lokacin da Kwankwqso ya dawo sai ya gyara duk wasu kura-kurai da yai a baya domin ta zame masa izina mai girman gaske a wannan lokacin. Sai ya zubar da abokai ya ɗebi ƴaƴan Talakawa ya ɗau nauyin karatun su suka zama ababen kwatance a duniya. Waɗannan matasa sai ya xamana dasu da dangin su sun zama masoyan kwankwaso har da abokan su masu son su. Daga nan ya sace zuciyar matasa kowa ka taɓa sai yace maka kwankwaso ko yace Kwankwasiyya. Shi kansa bai san iya ƙarfin ɗariƙar sa ta Kwankwasiyya ba kamar yadda masana suka faɗa. Ta tabbata cewa yafi kowa masoya Talakawa a najeriya idan aka cire Muhammad Buhari a ƴan siyasan najeriya haka babu mai matakin sa a Jihar Kano, shi yasa ya tako har jihar ya kada gwamnan dake ci a lokacin domin duniya ta sani anyi zaɓe yaci amma saboda taken sa na "kashin birbiri ƙawanya-ƙawanya, yara ke son ka manya gari ke ala tsine'' Sai yasa aka hana shi aka mayarwa da wancan gwamnan. Ko a wancan karo da Buhari yazo na ɗaya a zaɓen primary na jam'iyyar Maja wato APC shine wanda yazo na biyu bayan da Buhari yazo na ɗaya. Bashi da buri daya wuce yaga ya reni Talakawan da basu san komai ba yaga sun zama wasu kuma sun ɗauki nauyin wasu. Wannan karon daya fito shugaban ƙasa babu wani matashi cikin kaso 90 na ɗari da ba suyi na'am da buri ba domin har kullum ana masa kyatata zaton zai kai Talakawa ga tsira. Wannan shine babban dalilin da Kwankwaso zai ga soyayyar da bai taɓa gani ba a kakar zaben bana. Akwai waɗanda za suyi shinkafa da wake mafi yawan su waken nasu kwankwaso ne akwai wanda kuma za suyi kwankwaso zallah. Ciki kar ku manta da Hausawa mazauna Lagos da garin inyamurai wanda ya nuna fushin sa lokacin da aka taba su.