Shi wannan tsari na canjin kuɗaɗe a ƙasa abu ne wanda yake a dokan ce amma bisa yardar ahugaban ƙasa da shi kansa gwamnan babban bankin ƙasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya baiwa shugaba dama. Abunda mutane ya kamata su fahimta a nan shine: Gwamnan babban bankin kasa bashinda damar canza kuɗi bisa raɗin kansa har sai ya tuntuɓi shugaban ƙasa kuma ya yarda sannan ne za'a fara shirin canzawar daga baya sai a saka ranar dena karɓar tsaffin kuɗi ko kuma ace idan sun shiga ba zasu fita ba amma wannan zaɓi ne na shugaban ƙasar dake kan mulki, ya kuma danganta da irin kulawar da shugaban kasa kewa al'ummar sa da kuma yadda yake son su zauna lafiya ba tare da fargabar sabon canjin ba. Shi wannan gwamnan babban bankin bashi da iko sai dai ya karɓi umarni daga shugaban ƙasa duk son shi da ƙin sa da tsarin.
Zamu cigaba da kawo muku bayanan tsohon gwamnan babban bankin ƙasa kuma tsohon Sarkin kano Sunusi Lamiɗo Sunusi II.