Mataimakin Sufeto-Janar na ƴansanda, AIG, mai kula da shiyya ta 14, AIG Abdulrahman Ahmed, ya ce a shirye su ke su dakile matsalar tsaro a lokacin zaben da za a yi ranar Asabar a shiyyar.
Ahmed ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a jiya Alhamis a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua, Katsina, jim kadan bayan tafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa Daura.
A cewar AIG, ƴansanda a Katsina da Kaduna, jihohin da ke karkashin sa sun kammala shirye-shiryen su gabanin zaben ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
“A matsayina na AIG na zaben shiyyar, na zo na ga shirye-shiryen zaɓe da kwamishinan ƴansanda ya yi, ya yi ya yi aiki mai matukar kyau kyau.
"Na gamsu da tsarin da aka yi, kuma na kara abin da nake jin shine gibin, wanda suka yi daidai da shi, kuma ina ganin komai ya kankama.
“Ya ce yansanda sun samu kwarin guiwa, musamman da kokarin Sufeto Janar na ƴansanda (IGP), Usman Baba-Alkali.”