Sanatan yankin Kano ta Kudu, Kabiru Ibrahim Gaya, yace ya karɓi ƙaddara akan sakamakon zaɓen shekarar 2023 da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata, wanda a wannan rana sakamako ya nuna cewa, Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, na jam'iyyar NNPP ne yayi nasara, kamar yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta bayyana.
Gaya wanda ya shafe tsawon shekaru 16 yana wakiltar yankin, ya taya abokin karawar tasa, Kawu Sumaila, murnar bisa wannan nasara da ya samu, ya kuma tabbatar da cewa ba zai kalubalanci zaɓen a gaban kotu ba, domin shima sau hudu yana yin takara kuma yana cin zaɓe, amma sau daya aka taba kai shi kotu.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta bayyana Kawu Sumaila ma jam'iyyar NNPP a matsayin wanda yayi nasara, inda ya samu ƙuri'u 319,857 yayin da Kabiru Ibrahim Gaya na jam'iyyar APC ya samu ƙuri'u 192,518 a safiyar wannan rana.