Nan da ƙarshen watan Aprilun shekarar 2023 za'a dakatar da ƙarɓar duka kuɗaɗen tsofaffin kuɗaɗen kamar yadda shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana.
Bayan sanarwar da CBN ya bayar shekaran jiya na hana Bankuna karbar tsoffin kudi a yau shima shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kara tabbatar da hakan amma ya bada umurnin a cigaba da karbar iya tsohuwar 200 kadai inda ya umurci 'yan Najeriya da su gaggauta su maida tsoffin kudaden su CBN.
Kada ku manta CBN sun fara karbar tsoffin kudi tun a jiya Laraba sunce za su rufe karba daga gobe jumma'a.
Kusan duk ko'ina an daina karbar tsoffin kudade sai wurare 'yan kadan wasu jihohin tuni ko'ina an daina karba, duk da umurnin da wasu gwamnonin jihohi suka bayar.
Abunda ya kamata mu sani mu kuma kiyaye shine duk wanda kuka ga yana karbar tsoffin kudi to tabbas CBN zai kai su, CBN sunce daga gobe jumma'a za su rufe kuma bawai da zaran mutum yakai CBN a take zasu tura mishi kudin shi ba, dole sai sun dauki tsawon lokaci kafun su turawa Mutane kudin da suka kai wanda a kalla zai iya kaiwa makonni ko wata ko sama da haka.
Sannan ya kamata mu sani duk umurnin da Gwamnoni suke bawa al-ummar jihohinsu na su cigaba da karbar tsoffin kudi, duk wanda ya karba ya tara su a wurin shi har CBN suka rufe daina karbar tsoffin kudi ya sani cewa fa babu wani gwamnan da zai chanja mishi kudinshi karshe dai sai dai asara tahau kanshi shi kadai don haka ya kamata mu kiyaye.