Babban bankin ƙasa reshen jihar kano ƙarƙashin kulawar babban daraktan bankin ƙasa reshen jihar kano Alh. Umar, da shugabar sashen bayanai na babban bankin ƙasa Haj. Rakiya da kwamitin zaman lafiya na kano sun shirya taron masu hannu da shuni ɓangaren shafin sada zumunta da shuwagabannin ƙungiyoyi masu zaman kansu don tattauna batun wayarwa da al'umma kai kan harkar sabon kuɗi da babban bankin ƙasa ke gudanarwa.Babban bankin ƙasa reshen jihar kano ƙarƙashin kulawar babban daraktan bankin ƙasa reshen jihar kano Alh. Umar,
Haj. Rakiya
da kwamitin zaman lafiya na kano sun shirya taron masu hannu da shuni ɓangaren shafin sada zumunta da shuwagabannin ƙungiyoyi masu zaman kansu don tattauna batun wayarwa da al'umma kai kan harkar sabon kuɗi da babban bankin ƙasa ke gudanarwa.
Alh. Umar Ibrahim
wanda shi ke zama shugaban bankin kasa reshen jihar kano, ya bayyana yadda al'amarin ke kasancewa tsakanin su da al'ummar gari wanda suka haɗar da ƴan kasuwa da ƴan karkara inda yace ''wannan al'amari na canjin kudi dole ne mu karɓa kuma dole muyi amfani dashi kamar yadda shugaban ƙasa ya tabbatar tare da gwamnan bankin ƙasa Mr. GODWIN EMEFIELE, mun san cewa al'umma sun shiga ruɗani dangane da wannan al'amari kamar yadda muma muke ciki a yanzu saboda rashin fahimtar mu da al'umma suke yi duk da cewa akwai alfanu a cikin sauyin mai matuƙar amfani. Nima kaina ban iya transfer ba sai kwanan nan amma tsarin da CBN amma tsarin yayi dai-dai saboda za a rage barazana ga dukiyoyin al'umma da kuma faruwar sace-sace a gidajen al'umma''.
Haj. Rakiya tayi nata jawabin inda ta bayyana wasu muhimman al'amura da gwamnati zata cimma idan har wannan tsarin ya tabbata. inda tace ''Ƙasar mu tana da albarka amma mutanen ciki suna fama da son zuciya, wannan tsarin da gwamnati ta fiti dashi zai taimake mu matuka gaya kuma ababen da gwamnati zata cimma sun haɗar da : Samar da tsaro, ƙarancin kuɗi a hannu, bunƙasa tattalin arziki na ƙasa da sauran su'', mutane sun kasa fahimtar inda gwamnati ta dosa amma alhamdulillah da yawa an fara fahimtar inda muka dosa musamman mutanen jihar kano, wanda suke a jerin na biyu a kan harkokin kasuwa a najeriya wadda ina alfahari da jiha ta kuma cibiya ta''.
Amb. Ibrahim Waiya
shi ke zama shugaban kwamitin zaman lafiya na ƙasa reshen jihar kano, inda ya bayyan CBN a matsayin JAJIRTATTU kasancewar suna koƙarrin duk mai yiwuwa don ganin su fahimtar da al'umma inda aka dosa a wannann sabon tsari, duk da cewa wannan shine karo na farko da suka nemi shawarwarin Kungiyoyi masu zaman kansu saɓanin yadda suke a baya na tsara abubuwan su da suka gabata wanda suka shafi alumma kai tsaye. Ya kuma unarci mahalarta taron kan su tabbatar sun watsa wannan tsarin da kuma fahimtar dasu duk wata saƙara da babban bankin ƙasa ke nufi a kansu.
Shugaban babban bankin kasa reshen jihar kano Alh. Umar Ibrahim tare da Shugaban shafin labarai na Raihanaa.com.ng Cmr. Bashir A Bashir