Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Legas.
Sakamakon karshe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana a yau Litinin ya nuna cewa Obi ya samu kuri’u dubu 582,454, inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Tinubu wanda ya samu kuri’u dubu 572,606.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya zo na uku a zaben da kuri'u dubu 75,750.
Jaridar RAIHANA ta ruwaito cewa Legas jiha ce da ake ganin tana daya daga cikin wuraren da Tinubu ke da karfi.