Rundunar sojin kasar nan ta bayar da layukan wayoyin da za a tuntube ta domin sanar da duk wani hali na rashin tsaro yayin babban zaben kasar nan da za'ayi.
Rundunar ta bayyana layukan wayar da za a kira ta a kowace jiha don sanar da ita halin da ake ciki a shafinta na Twitter a Talatar nan.