Mai girma Gwamnan jahar jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya tabbatar da nadin Alh Hameem Nuhu Muhammad Sunusi a matsayin Sabon sarkin Dutse na 20.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da majalissar masarautar ta Dutse fitar.
Majalissar ta ce
Masu zaben sarki guda bakwai a masarautar Dutse sun zabi Muhammad Hameem a matsayin sabon Sarkin Dutse da kuri’u bakwai daga cikin ‘yan takara uku da suka nemi kujerar sarauta.
Wakilin Nasara Radio a jahar jigawa Muhammad Sa'idu Limawa ya rawaito cewar.
Sanarwar da Majalisar Masarautar ta fitar ta ce an mika sunan zababben Sarkin ga Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa wadda ita ma ta amince da zabin da masu zaban sarkin sukayi.
Sanarwar ta ce Majalisar Sarakunan ta aike da sunan Muhammad Hameem da sauran ’yan takara biyu ga mai girma Gwamna Muhammad Badaru Abubakar domin neman amincewarsa.
Daga bisani Gwamnan ya amince da Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse.
Alh Hameem Nuhu Muhammad Sunusi ya kasance dane ga marigayi Sarkin Dutse DR Nuhu Muhammad Sunusi wanda ya rasu a ranar talatar da ta gabata bayan gajeriyar jinya da yayi.
Muna tafe da cikakken rahoto a labaranmu na gaba.