Sanata Ahmad Lawan ya koma kujerar sa ta Sanata a Yobe.
February 27, 2023
0
Shugaban Majalisar Dattijai na najeriya Ahmad Lawan ya koma kujerar sa ta mulki a jihar Yobe bayan da ake ta cecekuce kan komawar sa kasancewar ana ganin kamar ya taka doka ko kuma anyi masa afarma ya koma kankujerar sa, wanda hakan yasa wasu ƴan najeriya ke ganin cewa har yanzu akwai almundahna da alfarma a cikin shari'ar najeriya wanda hakan ne ke karyar da gwiwar duk wani Talaka dake ƙasar najeriya. Wata majiya tace ya danganta da yadda yake mu'amalantar al'ummar sa da kuma yadda aka gudanar da zaɓen a yankin sa shin yana kyautata musu ko kuma ya fito da kuɗi dake musu wahala ya basu suka zaɓe shi?? Wannan shine babban abun tambaya.
Tags