A wani sako da ta wallafa a shafin ta na Twitter a juya Litinin da daddare, INEC ta ce “labarin ƙarya” ne.
Hukumar ta ƙara da cewa babu wani shiri kuma ba za ta ɗage zaɓen ba.
INEC ta kuma nanata cewa zaben shugaban ƙasaƙasa da na ƴan majalisun tarayya zai gudana ne a srane 25 ga watan Febrairu kamar yadda a ka tsara.
Haka shi ma zaɓen gwamna da ƴan majalisun jiha zai gudana a ranar 11 ga watan Maris kamar yadda aka tsara.