Mun gano kakan mu yana da kuɗin da suka kai kimanin nera miliyan ɗari takwas da hamsin 850,000,000.
Wasu yara sun kai ƙarar kakan su kotu bisa zargin shi da boye kudin da zai hana su shan wahala wanda adadin su ya doshi biliyan ɗaya.
Lauyan masu ƙara ya gabatar da ƙara inda yace ''ya maigirma mai shari'a Mal. Abubakar mutum ne daya kai kimanin shekaru 76 a duniya kuma mahaifi ne ga uban su Sadiq, Hafsat, Murja, isma'il, Muhammad, Yahya, da Abdullahi, bayan mutuwar mahaifin su sun kasance cikin wahala da tashin hankali na rashin abun duniya kuma duk da haka basu yada kakan su Mal. Abubakar ba sune suke kula dashi suke yi masa duk wani abu da Mahaigin su yake masa kafin ya bar duniya, sana'o'in da suke yi ba masu karfi bane don da kyar suke kai wayewar gari tare dashi, kwatsam! sai aka sanar da canjin kuɗi a ƙasa kuma muddin ba'a kaisu banki kafin ranar da aka kayyade ba to lallai ko nawa ne da mutum anyi asara sun zama yayi, hakan ce tasa Mal. Abubakar ya kira ɗaya daga cikin su ya bayyana masa sirrin sa na ma'ajiyar sa koda ya duba ya gano kuɗaɗen sai ya kira ƴan'uwansa ya shaida musu nan fa suka nuna lallai a ɗauko kuɗin nan ayi duk wani abu daya kamata dasu amma sai Mal. Abubakar ya nuna bai yarda ba kuma ya fara zage-zage kamar yadda idan aj fusata shi yake yida suka ga baza su iya yimai ta karfi ba sai suka kawo shi ƙara gaban kuliya manta sabo domin ta karɓi kuɗin nan ta basu shi su fara sana'a''.
Zamu kawo muku cigaban wannan shari'a mako mai zuwa.
Daga shafin Raihana
ku cigaba da bibiyar mu.