DALILAN DA SUKA SA SHUGABA BUHARI DAUKAR FANSA AKAN GWAMNONIN APC
Sannin kowa ne dai yanzu Gwamnonin APC 'SUN KARAYA' bisa ga matakan ba sani ba sabo da Shugaba Buhari ya dauka akan su, musanman na hana anfani da kudi wajen zabe, ta hanyar dakile tsaffin kudaden da suka tanada don aikata ta'addancin zabe.
AYUKKAN RASHIN MUTUNCI DA GWAMNONIN APC SUKA AIKATAWA SHUGABA BUHARI;
1- Bayan lashe zaben 2015, Shugaba Buhari Ya zaci Gwamnonin APC Masu tsoron Allah ne irin sa, don haka sai ya dinga SAKAR MASU BILIYOYIN KUDADE (State Budget Support,
Bailout,
Paris club refund, Anchor Borrowers, FG-CARES, COVID-19 Special grants da sauran su) Domin ayiwa TALAKAWA aiki, amma sai labari yazo masa cewa Gwamnonin sun sace wayannan kudade sun gina rijiyoyi sun boye sunki yi wa talakawa aiki, bayan jahar BORNO duk wata jaha ta APC da aka ga Gwamnan su yayi aiki toh BASHI NE YA CIYO Yayi aikin, Amma Kudin da Buhari ya bashi na can ya boye cikin rami. Wannan labarin ya batawa Buhari rai , sai kawai akaga yayi Yayi kyacci baice komai ba....lokacin ba'asan abinda yake kullawa ba a zuciyar sa.
2- Rashin mutunci na biyu shine yadda Gwamnonin APC suka mayar da kudaden kananan hukumomi tamkar kudin Gado, sacewa kawai sukeyi kamar ba zasu mutu ba. Kokarin Shugaba Buhari na aba Local Government kudaden su bai yi nasara ba, wayannan Gwamnoni sun hana, sanadiyar haka talauci da kiddinaping ya karu a kasa. Wannan ma yasa ran Shugaba Buhari ya baci..
3- Rashin mutunci na ukku da Gwamnonin APC sukawa Shugaba Buhari shine lokacin zaben shugabanin APC na kasa, cikin kujeru sama da 70, kujera daya tak suka ba Buhari, a matsayinsa na SHUGABAN KASA (Don tsabar RAININ WAYO), sauran kujera 70 da wani abu duk Gwamnonin APC suka nada su.... Ran Buhari Ya baci Yayi kyacci.., nan ma ba a fahinci abinda yake nufi ba
4- Rashin mutunci na hudu da Gwamnonin APC sukawa Shugaba Buhari Shine akan tsayarda yan takarkari a jahohin su; irin kujeran Gwamna, Sanata, Reps da sauran su. Nan ne Gwamnonin APC Sukayi wa Shugaba Buhari Ta'addancin da ko BELLO TURJI albarka; DUK WANI NA KUSA DA Shugaba Buhari Ba Wanda Gwamnonin APC Suka bari yakai labari. Misali a jahata ta Kebbi, manyan Yaran Buhari SUNE SANATA YAHAYA ARGUNGU da MINISTAN SHARI'A ABUBAKAR MALAMI, .. Gwamnan APC Na Kebbi duk sai da ya MUNAFINCE SU Ya hanasu takara a APC. Labari yakaiwa Buhari cewa Gwamnonin APC sun kashe masa yara a jahohin su; Buhari ya sake yin Kyaci...ba a san abinda yake nufi ba
5- Rashin mutunci na biyar shine yadda Shugaba Buhari ya kayar da girmansa, Ya fadi kasa yana rokon GWAMNONIN APC Cewa SUWA ALLAH SU TAIMAKA MASA SU BARI YA TSAIDA DAN TAKARAN SHUGABAN KASAN DA ZAI GAJESHI, Wanda ya yadda da ADALCIN SA Shugaba Buhari Yace:
"Ban sa baki ba lokacin da kuka tsaida wayanda zasu gaje ku, kuwa Allah ku bari in tsaida wanda nike so"
GWAMNONIN APC Sukace yayi kadan, sukaje sukasawa kujeran Shugaban kasa ganye cewa ta sayarwace, Dan-Boda (Tinubu) yaji Labari dama ya na da kudin sa yazo ya saya ya biya su. Shugaba Buhari na kallon su...ya sake yin kyaci tare da girgiza Kai.
YADDA SHUGABA BUHARI YA YAYIWA GWAMNONIN APC KWANTON BAUNA
Kasancewar shugaba Buhari tsohon soja ne dake da dibarun yaki kala kala, sai yayi anfami da dibaran yaki kala daya tak:
(1-) Idan abokin gaba( enemy) ya fara bude wuta, yana da kyau kayi abinda ake kira da yaren soja "TAKE COVER" ma'ana ka sami inda zaka boye; yin haka zai baka fa'ida 3:
1- zaka fahinci inda harsashi ke fitowa TARGET
2- Akawai yiwuwar harsashin abokin gaba ya Kare kafin ka fara mayar da martani
3-Zaka fahinci irin makaman da abokin gaban ka ke dasu, ta haka zaka samu damar sanin irin martanin da zaka mayar.
Yanzu shugaba Buhari ya gano TARGET Idan harsashi ke fitowa; ( GWAMNONIN APC)
Ya gano harsasan su ya Kare ( Sun ruga a guje Supreme Court domin suma suyi TAKING COVER)
Ya gane irin makamam dake hannun su ( TSAFIN TAKARDUN NAIRA, YA DAKYILE SU)
Ya yanke shawara akan makamin da zai mayar da martani domin samun galaba akan su ( SABBIN TAKARDUN NAIRA)
ADDU'AR KARSHE
Tsakanin Buhari da Gwamonin APC duk Wanda yafi wani gaskiya ALLAH YA BASHI NASARA, Duk Wanda ke wanga fada don Kare kudin da ya sata, ALLAH ya tona masu asiri, Ya hana su nasara.
DA KARSHE, INA ROKON ALLAH YA ZABAR MUNA MAFI ALHERI; Daga Sama har kasa, daga ko wace jam'iya.