Gurfanar da É—an takarar sanatan Kano-ta-Tsakiya na jam’iyyar APC, a ranar litinin ne karar da dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya na jam’iyyar APC, Abdulkarim Saleh Abdulsalam a gaban mai shari’a Mohammed Nasir Yunusa na babbar kotun tarayya da ke Kano ya sake samun tsaiko, biyo bayan sauya lauya da yayi a ranar litinin É—in.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar.
A cewar sanarwar, wannan ne karo na shida da a ka dage gurfanar da Abdulsalam, wanda aka fi sani da A.A Zaura.
Da aka kira Æ™arar, Basil Hemba wanda ke rike da takaitaccen bayanin Ahmed Raji, SAN, ya shaida wa kotun cewa su ne sabon lauyan wanda ake kara kuma suna bukatar lokaci don nazarin shari’ar, don haka ya nemi a dage zaman.
Lauya mai shigar da kara, Aisha Tahar Habib ta ki amincewa da bukatar a dage sauraron karar, amma kotun ta soke ta bisa hujjar cewa sabon lauyan na da hakki a karkashin doka ya yi nazari kan lamarin kafin ta nutse cikin lamarin.
Saboda haka, Mai shari’a Yunusa ya dage sauraron karar zuwa ranar 1 ga Maris, 2023 domin gurfanar da shi a gaban kuliya.
Ana tuhumar Zaura ne a gaban kuliya bisa zargin damfarar wani dan kasar Kuwait kudi dala miliyan $1,320,000 bisa zarginsa da cewa shi ma’aikaci ne a Dubai, Kuwait da sauran kasashen Larabawa.