Buhari dai yazo ranar Litinin inda ya dira a gidan Sarki daga bisani ya wuce gadar sama ta shataletalen Hotoro inda a nan aka samu wasu sukaiwa shugaban ihu kuma ana zargin wasu sun yi zagi a cikin maganganun nasu, wanda dalilin haka ne yasa hukumar take bi take kama duk wanda suka fito a wani faifan bidiyo da aka ɗauka inda take bi ɗaya bayan ɗaya take kama waɗannan matasa. Ƙungiyar Better Tomorrow Dakata wadda ke zama uwa ga wannan matashi tayi kira da a sassauta masa ta hannun Isma'il Isah Dakata
Yanzu haka yana komar DSS saboda ya yiwa Buhari ihu. Ƙungiyar Better Tomorrow Dakata.
February 03, 2023
2
Matashi mai suna Faisal Ɗan asalin ƙaramar hukumar Dakata yana ɗaya daga cikin fusatattun matasan da sukaiwa Buhari ihu ranar daya zo kano domin buɗe wasu muhimman ayyuka da gwamnatin kano ƙarƙashin shugabancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje tayi.
Tags